Wasu Bama-Bamai Sun Fashe Da kashe Mutane Da Dama A Kasar Somaliya


4bmt4a64fef904kiu4_800c450

 

Rahotanni daga kasar Somaliya sun bayyana cewar wasu motoci dauke da bama-bamai sun fashe a kusa da filin jirgin saman Mogadishu babban birnin kasar Somaliya lamarin da yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunana wasu mutane.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo wasu majiyoyin ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Al-Shabab suna cewa su ne suka kai harin a wannan yanki wanda ke da gine-gine na gwamnati, ofisoshin jakadanci da kuma kamfanonin sadarwa bugu da kari kan helkwatar dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya jiyo wani jami’in ‘yan sandan birnin na Mogadishu Mohamed Ahmed yana cewa yana cewa mota ta farko ta fashe ne a wajen binciken motoci da ke kusa da sansanin da dakarun kungiyar Tarayyar Afirka suke lokacin da dan kunar bakin waken da ke cikin motar lamarin da yayi sanadiyyar kashe ‘yan sanda uku da suke ganin ginin.

Har ila yau mota ta biyun kuma wacce ta nufo asalin kofar helkwatar, ta fuskanci bude wuta daga sojojin da suke ganin ginin, lamarin da ya tilasta wa dan ta’addan da ke cikinta tarwatsa ta kusa da wani.

You may also like