Shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, a ranar talata yace wasu daga cikin bankuna a Najeriya sun kusa karyewa sakamakon aiyukan rashin dacewa na wasu mutanen.
A wata tataunawa tsakanin Magu da shugaban kungiyar kiyaye hakkin jami’an bankin Najeriya a ranar talata a jihar Legas, shugaban hukumar yaki da rashawan ya hori jami’an da su taimaka ta hanyar samar da bayanai ga hukumar.
“Dole ne muyi kokarin ceto kasar nan
Da yawan bankunan nan sun kusa karyewa.
Na san akwai tambayoyin da b azaku iya tambaya ba, ballantana in sun shafi wasu mutane, amma Idan kuka bamu bayanai akan mutanen, mu zamu iya.
Idan akwai manyan matsalolin da zasu iya shafar bankunan ku, zaku iya bamu bayanai, balle yanzu da zaben ke gabatowa.”
“Bana son in dinga tuhumar bankuna saboda wasu ‘yan ta’adda saboda yin hakan zai iya kawo nakasu ga tattalin arzikinmu.
Zai iya hana masu sa hannayen jari zuwa kasar.”
“Kowane banki na iya samun matsala, komai shaharar shi Shi yasa muke so muga baku fada matsala ba.
A shirye muke don hada kai daku don ganin cigaban tattalin arzikin kasar nan.
A shirye muke don ganin mun karbo muku basussukan da kuke bi amma fa in kun dage da aiyukan ku.” Inji Magu