Wasu da ake zargin fulani makiyaya ne sun yi musayar wuta jami’an sojoji da suka fito daga Birged ta musamman da a ake kira 707 dake Makurdi a jihar Benue a ranar Talata.
Olabisi Ayeni, mai magana da yawun birged ɗin shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar a ranar Alhamis.
Yace mutanen da ake zargi na shirin kai hari ne kan wata gonar kifi mallakar gwamnan jihar Samuel Ortom.
Ayeni ya ce an samu nasarar kama biyu daga cikin maharan.
Sanarwa ta ƙara da cewa sojojin rundunar ne suka hangi mutanen lokacin da suke gudanar da sintiri a kan hanyar Gbajimba zuwa Iyiodeh dake ƙaramar hukumar Guma ranar Talata 6 ga watan Faburairu.
Bayan da suka hangi sojojin dake sintiri mutanen sun ɓude wuta akan sojojin inda suka samu nasarar fatattakar su tare da kama biyu daga ciki.