Gwamnatin tarayya tace wasu dagacikin yan matan Chibok 82, da da aka ceto suna bukatar aikin tayata.
Ministar harkokin mata da walwalar jama’a Hajiya Aisha Jummai Alhasan ta bayyana haka a jiya Alhamis tace “yan matan Chibok 82, da aka ceto yanzu haka ana tantance koshin lafiyarsu,wadansu daga cikinsu suna bukatar aikin tiyata, kuma za’a kammala aikin cikin makonni biyu. ”
Ministar tace ana cigaba da tattunawa dan ganin an sako ragowar yan matan da Boko Haram ke tsare dasu.
A kalla yan mata 113 cikin 276 da aka sace daga makarantar sakandiren garin Chibok dake jihar Borno a watan Afirilun shekarar 2014, ke can rike a hannu yan Boko Haram.
Lokacin da takewa yan jaridu bayani ministar tace” Ana ci gaba da tattaunawa domin musayar ragowar yan matan da yan kungiyar Boko Haram da gwamnati ke tsare dasu, baza mu iya kyalesu su cigaba da zama ba.
“Bama bukatar bada hakuri ko yin dana sani kan musayar yan Boko Haram da yan matan mu, zamu sake yi,idan bukatar yin hakan ta taso.”
Alhasan tace tuni aka hada yan mata 21 da aka ceto tun da fari da iyayensu
Tace yan matan suna tsoron komawa garin Chibok saboda halin damuwa da suke ciki.
Mun tattauna da iyayen yan matan da kuma su yan matan inda suka amince gwamnatin tarayya ta mai dasu makaranta ta kuma cigaba da kula dasu,saboda suna tsoron komawa garin Chibok.