Wasu gungun mahara dauke da manyan makamai sun farma wani ofishin ‘yan sanda a kauyen Eika da ke karamar hukumar Okehi a jihar Kogi a tarayyar Nigeriya, inda suka kashe mutane hudu kuma biyu daga cikinsu ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi Abdullahi Chafe ya bayyana cewa: Maharan sun farma ofishin ‘yan sandan ne da misalin karfe daya na daren Juma’a dauke da manyan makamai, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda biyu tare da wani mutum da ake tsare da shi a ofishin, sannan suka kona ofishin.
Bayan nan maharan sun nausa zuwa gidan shugaban kungiyar bunkasa ci gaban al’ummar kauyen Eika mai suna Sadiq Obomi, inda suka kashe shi, sannan suka tsere a cikin wasu motoci biyu da suka zo da su.
Wata majiya a kauyen na Eika ta bayyana cewa: Maharan da yawansu ya kai mutane kimanin goma dauke da manyan bindigogi sun shafe tsawon sa’o’i biyu suna cin karensu babu bambaka kafin suka fice daga kauyen a cikin motoci biyu.