Rahotanni daga Kaduna sun tabbatar da cewa wasu mahara sun sace Sarkin garin Anchuna da ke karamar hukumar Zangon Kataf , Yohanna Kuka a yayin wani farmaki da suka kai kauyen.
Basaraken dai, dan Uwar fitaccen malamin addinin Kiristan nan ne, Rabaran Mathew kukah. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun dira kauyen ne da misalin Karfe Tara na dare inda suka zarce zuwa gidan basaraken kai tsaye kuma suka rika harbi sannan suka arce da shi tare da wani mai tsaron lafiyarsa.