Wasu Mahara Sun Kashe Akalla Mutane 10 A Kogi


Wasu mahara wadanda ba a san ko su wane ne ba sun kai wani mummunan hari a garin Kpanche da ke cikin karamar hukumar Bassa a jihar Kogi inda suka kashe akalla mutane biyar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Janga ya ce, rundunar tsaro ta samu nasarar kashe maharan guda biyar tare da fatattakar sauran tare da kwato wasu makamai.

Ya kara da cewa maharan sun kona wasu gidaje da wasu kadarori a yayin harin wanda ya hada har da Motoci, Babura da kuma Keken Napep. Har yanzu ba a tantance makasudin kai harin ba.

You may also like