Wasu Mahara Sun Yi Awon Gaba Da Matan Aure Uku A Jihar Kaduna


A wani hari da wasu mahara suka kai Kauyen Maganda, da ke karamar hukumar Birnin Gwari, sun yi garkuwa da matan aure uku a gidan mijin su Alhaji, Makwalla.

Idan ba a manta ba makonni biyu da suka gabata babban hafasan sojojin Najeriya Tukur Buratai ya ziyarci Birnin Gwari sannan ya bude sabuwar sansanin sojoji a yankin.

Kamar yadda wani jami’in tsaro na sa kai ya fadi wa ‘PR NIGERIA’ maharan sun dade suna aiko da sako kauyen cewa suna nan zuwa , za su kawo musu hari.
” Sun iso wannan kauye ne da misalin karfe 1:30 na dare sannan suka yi ta haba bindiga ta ko ina a kauyen. A hakane daga nan suka far gidan shi Alhaji Makwalla, suka yi garkuwa da matan sa uku. Daga baya sun saki mata daya da sakon lambar wayar da za a kira su da shi.”

Ba a rasa rai ko daya ba a harin sai dai wani matashi ya sami rauni.

You may also like