Wasu makiya Musulunci da ba a san ko su waye ba sun yi yunkurin kona wani Masallacin Juma’a a garin Toronto na kasar Kanada inda jami’an kashe gobara suka kashe wutar kafin ta kama sosai.
Sanarwar da Hukumar Kashe Gobara ta Toronto ta fitar na cewa, sun samu labarin kamawar wuta a Masallacin Juma’a da ke kan titin Weston a garin na Toronto kuma an aika motocin kashe gobara 3 inda suka kashe wutar kafin ta yadu zuwa cikin Masallacin.
‘Yan sandan Toronto sun fara gudanar da bincike kan lamarin inda suka ce, an zuba man fetur a saman rufin Masallacin amma wutar ba ta yi barna ba.
Kakakin ‘yan sandan Toronto Victor Kwong sun fara bincike game da kokarin kona Masallacin da aka yi.