Wasu masoya sun kashe jaririyar da suka haifa


Nigeria-Police-Recruitment-2016

Ƴansanda a Gwarinpa suna tsare da wasu masoya biyu bisa zargin bawa jaririyar da suka haifa ƴar wata 6 wani abun sha da yayi kama da guba.
Majiyar ƴansanda tace sun aikata haka a ranar Talata da daddare.
Majiyar jaridar Dailytrust tace mutumin mai suna Abdullahi ɗan shekara 23 da masoyiyarsa Hasiya mai shekaru 17 sun haɗa baki sun kashe jaririyar saboda sun haifeta batare da aure ba.
Majiyar ta ƙara da cewa Hasiya ta gayyaci Abdullahi kan yazo ya duba rashin lafiyar da jaririyar ke fama da ita.
“Abdullahi yabata kuɗi ta sayi magani a wani wurin sai da magani dake kusa,bayan sun bawa jaririyar maganin sai ta fara aman wani abu mai kumfa” majiyar tace
Mazauna unguwar sun sanar da ƴansanda abin da yafaru.
Jami’in ƴansanda na yankin CSP Nuruddeen Sabo yace waɗanda ake zargin ba tare suke zaune ba inda ya bayyana su a matsayin saurayi da budurwa.

Yace binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa masoyan sun haɗa baki inda suka bawa jaririyar tasu wani abu mai ruwa da ake zargin maganin ɓera ne ko kuma maganin ƙwari na fiya-fiya.

yace anji warin maganin a jikin gawar jaririyar, tuni dai aka kai gawar jaririyar asibiti don cigaba da bincike.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like