Wasu Masu Gonaki Na Neman A Biya Su Diyya A Kano
Ko da yake, a rangadin da ministan sufurin kasar Rotimi Ameachi ya kai kimanin makonni biyu baya domin ganin yadda aikin ya fara gudana, ya ce gwamnati ta kammala biyan kowa diyya, amma daga bisani al’umomin na ci gaba da bayyana rashin gamsuwa.

Dayyabu Umar na cikin daya daga cikin dubban manoma da aikin shimfida layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna ya ratsa da gonakin su, wadda gwamnatin Najeriya ta baiwa wani Kamfanin kasar China akan biliyoyin dala, ya kuma ce an bai wa mutum biyu hakki, wasu kuma ba a ba su ba, an ce kasa ta gwamnati ne, ba ta tallaka ba ce.

Sai dai Alhaji Sagir Sulaiman da ke zaman manajan shiyyar arewa maso yamma na kamfanin dake kula da kadarorin hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya ya ce akwai matakan da suka bi wajen biyar diyyar.

Amma wadannan al’umomin da wannan aikin hanyar jirgin kasa ya tafi da gonakinsu, sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya shiga cikin wannan lamari.

A watan Yulin bara, shugaba Buhari ya kaddamar da aikin layin dogon, wanda ya tashi daga Kano zuwa Kaduna, wanda har ila yau zai hade da layin dogo na Abuja.

You may also like