Wasu matasa a unguwar Narayi dake karamar hukumar Chikun a Kaduna sun cinnawa ginin wata caji ofis din yan sanda wita da kuma wata coci dake unguwar.
Rikicin ya fara ne sakamakon mutuwar wani yaro dake aiki a cocin, Babatunde Shitu limamin cocin shi aka da alhakin mutuwar yaron.
An ce yaron ya na yin wani aiki ne da Shitu ya saka shi yi amma sai ya fada ruwa kuma ya mutu sanadiyar haka.
An rawaito cewa limamin cocin ya garzaya ya zuwa ofishin yan sanda mafi kusa domin ya kai rahoton faruwar lamarin.
Amma matasan sai suka tattaro kansu suka kona cocin da kuma wata mota mallakin wani mamba na cocin da aka ajiye ta a harabar cocin.
An kona ofishin yan sandan ne bayan da matasan suka dage kan cewa sai an basu limamin cocin wanda aka dauke shi ya zuwa ofishin yan sanda dake Barnawa domin tsare lafiyarsa.
Mukhtar Aliyu mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce tuni aka kama mutane biyar da ake zarginsu da hannu a lamarin.