Wata kotu a Legas ta fara sauraren karar da aka shigar a kan wasu matasa uku bisa tuhumarsu da yaudarar wata yarinya ‘yar shekara bakwai wajen yi mata fyade a unguwar Adaraloye da ke yankin Ikorodu a jihar.
Matasan da ake zargin, suna sana’ar Birkila ne inda kuma aka ba su aiki a cikin gidan da iyayen yarinyar ke haya a unguwar ta Adaraloye. A bisa bayanan da kotu ta saurara daga daya cikin matasan wanda ya amsa laifin, ya nuna cewa sun yaudari yarinyar ce ta hanyar yi mata alkawarin ba ta wasu kudade inda ta amince suka sanya ta cikin wani daki a cikin gidan.
A cewar matashin mai suna Osholo Samuel, a yayin da suke yi wa yarinyar fyade ta rika yin kuka inda ya nemi ‘yan uwan nasa kan su dakatar da yin hakan don gudun kada ta mutu wanda a cewarsa, ‘yan uwan ta’addancin nasa sun ki amincewa da shawararsa inda ma, suka rufe mata baki. Mai Shari’a a kotun, Mrs A. A. Oshoniyi, ta bayar da belin matasan a kan Naira 200,000.