Wasu matasan Arewa sun nemi, Atiku, Lamido da sauransu da su barwa Dankwambo takarar shugaban kasa 


Matasan Arewa ƙarƙashin wata kungiya da ake kira Arewa Youth Coalition sun yi kira ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, tsohon shugaban kwamitin riko na jam’iyar PDP, Ahmad Muhammad Makarfi  da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido kan su janye aniyarsu ta takarar shugaban kasa.
Amma gamayyar kungiyoyin matasan sun nemi ƴan takarkaru dake takara a jam’iyar PDP da su goyi bayan gwamnan jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo.

Matasan na Arewa sun ce Najeriya tana bukatar shugaba mai ƙarancin shekaru da kuma ƙwazo kamar Dankwambo wanda ya nuna misalin haka.

Da yake magana a wurin gangamin taron da aka shirya a Kaduna domin nuna goyon baya ga Dankwambo shugaban gamayyar, Kwamared Abdullahi Muhammad Jika yace “kowa ya sani a ƙasarnan cigaban mu bai kai inda ya kamata ace mun kai ba dalilin da yasa muke kiran gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya zo ya yi takara domin ceto ƙasarnan daga tarin matsalolin da take fama da su.”
“Mun zaɓi Dankwambo saboda mun ga irin aikin da yayi a jihar Gombe. Shine ɗan Najeriya da ba ya nuna ƙabilanci yana da maganin matsalar tattalin arziki da kuma ta tsaro dake damun ƙasarnan kuma zai iya kai ƙasarnan ga tudun mun tsira.

“Saboda haka muke kiran sauran ƴan takarkaru dake cikin jam’iyar da su saka buƙatar su a gefe guda su goyi bayan Dankwambo da duk kannin abinda suke dashi, da mutanen da suka sani domin PDP tamkar iyali ɗaya muke.”

You may also like