Wasu mutane sun buɗe wuta kan ayarin motocin matafiya a jihar Borno


boko-haram

Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar Boko Haram ne sun buɗe wuta kan jerin ayarin motocin matafiya akan hanyar Maiduguri zuwa Damoba a jihar Borno.

A yarin motocin da suke tafiya kudancin jihar daga Maiduguri na samun rakiyar jami’an tsaro, motocin dai suna taruwa ne a Molai dake wajen birnin na Maiduguri inda harin ya faru.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa sa’o’i kaɗan kafin motocin su kama hanyarsu, wasu ƴan bindiga suka bayyana suna harbin kan me uwa da wabi inda suka kashe mutane da dama tare da raunata wasu.

Har ya zuwa yanzu dai jami’an tsaro a jihar ba su bayyana adadin waɗanda suka jikkata ko suka rasa rayukansu a harin ba.

You may also like