Wasu mutane sun mamaye gidan yari a Jihar Benue


prison

Hukumar dake kula da gidan yari a jihar Benue ta tabbatar da cewa wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun mamaye gidan gonarta dake Jato Aka, inda suka kashe fursuna guda ɗaya mai suna Tersoo Agidi.

Mai magana da yawun hukumar gidan yari ta jihar Stephen Nwanchor ya fadawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Makurdi cewa harin ya farune ranar Asabar a gidan gonar.

Nwanchor yace wannan sabon gidan gona ne da aka bude a watan janairun 2017 maharan sun mamaye shi, sun lalata kayayyaki, sannan suka kashe mai zaman kaso guda daya..

Tuni dai aka kwashe ragowar masu zaman kason da suka rage zuwa garin Gboko har sai an kammala bincike kan musabbabin harin.

Tuni aka tsaurara matakan tsaro a dukkan gidajen yari da suke jihar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like