Wani abun takaici da ya faru a jihar Kaduna, wasu maza 8 sun yi ma yarinya ‘yar shekaru 13 fyade wanda aka bayyana daya daga cikinsu limamin masallaci ne wanda a halin yanzu yarinyar na dauke da cikin ‘yan biyu.
Shugaban gidauniyar Arridah Foundation, Malama Rabi Salisu ta shaida wa kamfanin Dillancin Labarai wato NAN a ranar Asabar da ta gabata a Kaduna cewa, an kawo karar wannan lamarin ga gidauniyarsu ne domin nema wa wannan yarinyar adalci.
Ta bayyana cewa, za su yi iya kokarinsu na ganin sun nemi taimako da bin karar a kotu har sai an hukunta masu laifin.
Lamarin da ya faru a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna, an bayyana cewa Limamin da aka ce yana daga cikin wadanda suka yi wa yarinyar fyade makocinsu ne.
Malama Rabi ta ce a shekarun su na wannan aikin, sun karbi kararraki da suka magance na fyade da tauye hakkin yara sama da 400 amma ba su taba samun irin wannan ba.
Ta bayyan cewa, “wannan abun takaici ne a ce maza 8 sun yi wa ‘yar sheakara 13 fyade. To yanzu ta samu juna biyu wanda a yanzu haka iyayenta na kokarin zubar da cikin don gudun tsangwamar jama’a.
“Wadanda suka yi mata fyade su 8 ne, ba a sani ba kila wani yana dauke da cutar HIV mai yiwuwa ya saka mata, ko kuma cututtuka da ake iya dauka sanadin fyade”.
Rabi Salisu ta bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta shiga tsakanin wannan lamarin tare da sarakunan gargajiya da kungiyoyin kare hakkin bil Adama don nema wa wannan yarinya adalci tare da iyayen ta da suke marasa karfi.
A bangaren mahainfin yarinyar Malam Mu’azu Shittu, ya bayyana cewa sun riga da sun shigar da karar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Ikara.
Kamar yadda ya bayyana, ya ce a baya bai yarda a zubar da cikin ba, amma an ba shi shawarar yin hakan domin ta yi kankanta da rike cikin, abun takaici ma babu daya daga cikin wadanda suka yi wannan ta’asa da zai iya daukar dauwainiyar cikin.
Yarinyar ta bayyana cewa, sun kira ta ne suka ba ta Naira 500 bayan ta dawo daga makaranta.
Da ta fito za ta je talla sai suka tare ta suka tilasta ta suka yi mata fyade.
Sun gargade ta da cewa kar ta gaya wa mahaifin domin za su kashe ta idan ta yi hakan inda a cewarta, ta ji tsoro ta ki fada.