Wasu mutanen sun sace sandar majalisar dattawa


An shiga rudani a majalisar dattawa bayan da wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka sace sandar majalisar a harabar majalisar da safiyar yau.

Mutanen su biyar ne suka shiga harabar majalisar lokacin da mataimakin shugaban majalisar Ike Ekweremadu ke jagorantar zaman majalisar.

Mutanen da suka haɗa da wasu manyan mutane biyu sun fice daga harabar majalisar ta cikin babbar kofar shiga majalisar.

Da fitar su ba suyi wata-wata ba suka shige cikin wata mota kirar Jeep dake jiran su a waje.

Sandan majalisar na da muhimmancin gaske a tsarin yin dokoki a majalisu tun daga matakin majalisar dokokin jihohi har ya zuwa majalisun tarayya.

A shekarun baya an sha samun yunkuri sace sandan a wasu majalisun jihohi dama na tarayya.

You may also like