Wani Rukunin Na Yan Najeriya Su 165 Sun Dawo Gida Daga Kasar Libiya 


A kalla yan Najeriya su 165 ne suka dawo gida daga kasar Libiya a yau Alhamis da misalin karfe 5 na yamma. 

Rukunin biyu ne na yan Najeriya su 258 suka dawo gida daga kasar ta Libiya dake arewacin Afirika. 

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na, Murtala Muhammad,dake Legas. 

Wadanda suka dawo gidan sun hada da maza 97, mata 54, yara 11  da kuma jarirai uku. 

Hukumar kula da yan cirani ta duniya tare da ofishin jakadancin Najeriya dake Libiya, suka dau nauyin dawo da mutanen gida. 
Mutanen sun samu tarba a bangaren  sansanin alhazai na filin jirgin daga jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa da na hukumar yaki da fataucin mutane ta kasa NAPTIP da yan sanda da kuma jami’an hukumar kai daukin gaggawa ta kasa NEMA.

Da yakewa yan jaridu jawabi Daraktan NEMA,Mustafa Maihaja yace, hukumar sa da hadin gwiwar hukumar kula da yan cirani ta duniya na aiki kafada da kafada don ganin an dawo da yan Najeriya da suka makale a kasar ta Libiya.

Biyu daga cikin mutanen da suka dawo sun fadawa NAN cewa sun shafe watanni shida a gidan yari bayan da aka siyar dasu a matsayin bayi. 

Sun godewa gwamnatin tarayya kan yadda ta taimaka suka dawo gida. 

An dai bawa kowannensu naira  17,100 kafin a mika su zuwa tashar mota ta Jibowu.
Kasar ta Libiya mai fama da rikici ta kasance wata hanya da mutane suke amfani da ita su tsallaka zuwa kasashen Turai.  

You may also like