Wasu gungun sojoji sun ce sun “kifar” da gwamnatin Turkiyya, bayan da suka mamaye muhimman wurare a biranen Istanbul da Ankara.
Sai dai Firai Ministan kasar Binali Yildirim ya ce gwamnati “na nan daram da gindinta, kuma matakin sojojin haramtacce ne”.
Gungun sojoji sun bayar da sanarwa ta gidan talabijin na NTV cewa sun kwace iko da dukkan kasar.
Mista Yildirim ya ce gwamnati ba ta amince da matakin ba.
An tsayar da zurga-zurgar ababan hawa da ke kokarin bi ta kan gadojin Fatih Sultan Mehmet a birnin Istanbul.
An dai kaddamar da yunkurin juyin mulkin ne a lokacin da shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan ya tafi hutu.
An yi hira da shi ta gidan talabijin inda ya yi kira ga magoya bayan sa su futo zanga zanga dan nuna goyon baya ga dimokradiyya.
Ya ce yunkurin juyin mulkin ba zai yi nasara ba.
Akwai kuma rahotanni dake cew ana kiraye kiraye a masallatai na cewa jama’a su futo tituna.
Mutane da dama sun futo tituna a birnin Istanbul, inda suke rike da totocin kasar.
Sojojin da suka yi juyin mulkin dai sun sanya dokar takaita futa.
Sanarwar da sojojin da suka shelanta juyin mulkin suka futar ta ce wata majalisa ce wacce ta kira ta zaman lafiya za ta jagoranci kasar, wacce za ta daidaita al’amura.
Za kuma a samar da kundin tsarin mulki cikin gaggawa a cewar masu yunkurin juyin mulkin.
Haka kuma an bada rahoton cewa wasu jirage masu saukar Aungulu na soja ya yi harbi a kan gidan talabijin din kasar.
An ji karar fashewar abubwa a birnin na Ankara.
Ana kuma samun rahotannin harbe-harben bindiga a Ankara, babban birnin kasar ta Turkiyya.