Wasu Sojojin Amurka 5 Sun Mutu A Kasar Siriya


 

Rahotanni daga kasar Siriya sun bayyana cewar wasu sojojin Amurka guda biyar da wasu dakarun sa kai na Kurdawa biyu sun mutu sakamakon fashewar wani abu a wani sansanin sojin hadin gwuiwa na Kurdawa da ke garin Hasaka dake arewa maso gabashin kasar Siriyan.

Rahotannin sun bayyana cewar an jiyo mummunar karar fashewar wasu abubuwa a sansanin sojin, inda daga baya aka tabbatar da cewa fashewar ta faru ne a cikin wani rumbu na makamai wanda yake karkashin iko da sanya idon sojojin Amurka ne.

Rahotannin sun jiyo wasu majiyoyin tsaro suna cewa fashewar dai ta yi sanadiyyar mutuwar wasu sojojin Amurka su biyar da kuma wasu dakarun sa kai na Kurdawan su biyu.

Shi dai garin na Hasaka yana yankin da Kurdawan kasar Siriyan suke da ke yankin arewa maso gabashin kasar Siriyan. Sojojin Amurkan dai suna ikirarin taimakon Kurdawan ne a fadar da suke yi da ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh da suke barazana wa yankunan Kurdawan.

You may also like