Wasu tambayoyi da lauya Bukarti ya nemi masu kare Buhari su amsa masa


Wani lauya, Audu Bulama Bukarti  mazaunin jihar Kano da yayi ƙaurin suna wajen kare hakkin bil’adama da kuma mutane marasa galihu ya jefawa masu yi wa shugaban ƙasa Muhammad Buhari makauniyar soyayya wasu jerin tambayoyi da ya kamata su riƙa yiwa kansu.

Tambayoyin da lauyan ya yi sun shafi abubuwa da dama kan halin da ƴan Najeriya suka samu kan su tun bayan hawan wannan gwamnati ta Baba Buhari kan karagar mulkin kasar nan.

Bukarti ya nemi jin amsoshin tambayoyin daga bakin masu kare shugaban.

Tambayoyin sune:

1-Shin Allah ne ya rufe boda ko Buhari?
2-Allah ne ya janye tallafin taki ko Buhari?

3-Allah ne ya janye tallafin mai ko Buhari?

4-Allah ne ya janye tallafin dala ko Buhari?

You may also like