Rahotanni daga Nijeriya sun bayyaan cewar wasu mutane 6 sun rasa rayukansu kana wasu daruruwan shanu kuma sun bace sakamakon wani harin da barayin shanu suka kai gundumar Kukoki da ke karamar hukumar Shiroro, na jihar Nija da ke arewacin Nijeriyan.
Shugaban karamar hukumar Shiroron Mark Jagaba ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) cewa harin dai ya dauki awanni hudu ana yinsa inda ya ce wasu fulani guda hudu da kuma wasu ‘yan kabilar Gbagyi guda biyu sun rasa rayukansu kana wasu da dama kuma ciki har da mata da kanana yara sun sami raunuka
Mr. Jagaba ya kara da cewa mutanen gundumar sun shaida musu cewa wasu mutane da adadinsu ya kai mutum 50 dauke da muggan makamai ne suka kawo harin inda suke bude wuta kan mai uwa da wabi inda ya ce bayan sun kashe mutanen har iya yau kuma sun yi awun gaba da shanu kimanin 700 da kuma wani adadi na tumaki da awaki da ba a tantance adadinsu ba.
Kimanin makonni ukun da suka gabata ma dai an kawo hari makamancin wannan da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 9 a wasu yankuna na karamar hukumar Shiroron.