Wasu ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin EFCC Dake Abuja


EFCC-AT-14

 

 

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai harin ta’addanci ofishin hukumar EFCC dake Wuse zone 6 a  Abuja.

Hakan ya faru a safiyyar yau Laraba inda  ‘yan bindigar dake dauke da bindigogi suka fara harbe-harbe a harabar ofishin.

Sai dai har zuwa yanzu hukumar ta ce ba ta san ko su waye suka kai harin ba

Wilson Uwujaren, Mai magana da yawun hukumar ya ce masu gadin ofishin sun fatattaki ‘yan bindigar, amma kafin sannan sun lalata motocin dake harabar ofishin.

Ya kuma ce ‘yan bindigar sun ajiye wata ambulan, wadda ke dauke da sakon barazana ga shugaban sashen da ke bincike a kan almundahana da ta shafi musayar kudaden waje, Ishaku Sharu.

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da hukumar ke zafafa bincike a kan wadanda ake zargi da almundahana da yin sama da fadi da kudaden gwamnati.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like