‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wani Ofishin ‘Yan Sanda, Inda Suka Kashe Sufeto Daya Tare Da Yin Awon Gaba Da Bindigu A Jihar Ekiti
Wani jami’in dan sanda mai mukamin sufeto ya rasa ransa a yayin wani farmaki da wasu ‘yan bindiga suka kai ofishin ‘yan sanda na yankin Ido-Ekiti dake karamar hukumar Ido/Osi a jihar Ekiti.
Lamarin wanda ya auku a jiya Juma’a, ‘yan bindigan sun kai su kimanin mugane 40 a yayin da suka kai farmakin, sannan kuma sun yi awon gaba da bindigu da dama.