Wasu yan bindiga sun kashe mutane biyar a jihar Plateau


Wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutane biyar a kauyukan Dantako da Nzharuvo dake gundumar  Miango a karamar hukumar Bassa ta jihar.

Terna Tyopev,mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar shine ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN faruwar lamarin a Jos ranar Juma’a.

A cewarsa lamarin da yafaru a daren ranar Alhamis ya bar mutane da yawa da munanan raunuka ya yin da aka lalata kayayyaki masu yawa.

“Jiya wasu yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari tare da kashe mutanen Irigwe hudu a kauyen Dantanko da kuma wani bafulatani a kauyen Nzharuvo dake gundumar Miango a karamar hukumar Bassa,” ya ce.

“Mutanen da suka mutu sun hada da Emmanuel Joseph,Christopher Joseph, Peace Joseph, Henry Audu and Samuel Isa.

“Tuni aka binne gawar Samuel Isa amma gawarwakin ragowar mutanen hudu an ajiye su a dakin ajiye gawarwaki dake Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Jos.”

Tyopev ya kara da cewa wadanda suka jikkata a harin har da wani yaro dan shekara hudu kuma  suna karbar magani Asibitin Enos dake Miango.

Ya ce ana cigaba da bincike domin gano wadanda ke da hannu a wannan mummunan aiki.

Harin ya faru ne lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ke ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar.

You may also like