Wasu yan bindiga sun kashe mutane hudu a jihar Plateau


Wasu yan bindiga a ranar Laraba sun kashe wasu ma’aikatan gini su hudu a kauyen Angwan Rogo dake yankin Jebu-Miango a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau.

Majiyoyi dake kauyen sun fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa, ma’aikatan na dibar yashi ne na wani aikin gini da suke lokacin da aka kai musu hari.

Da yake tabbatar da faruwar harin, Terna Tyopev, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya fadawa NAN cewa harin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe.

” Mun samu bayanan dake nuna an kai hari a kauyen Angwan Rogo, mun kuma tabbatar da cewar mutane hudu maharan suka kashe.

“Mun kuma iya tabbatar da cewa mutanen leburori ne dake hakar ya shi na wani aikin gini da suke yi lokacin da aka kai musu harin, ” ya ce.

Tyopev ya yi ikirarin cewa fulani makiyaya ne suka kai harin

You may also like