Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da matar Kwamishina da kuma yayansa uku a jihar Zamfara


An sace mata da kuma yaya uku na Abdullahi Bore, wani kwamishina a jihar Zamfara.

Wasu yan bindiga da ba’a san ko suwaye ba , su suka shiga gidansu dake kauyen Bore a karamar hukumar Zurmi ta jihar da farkon safiyar ranar Talata.

Kwamishinan ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin inda ya ce wasu yan uwansa uku suma an sace su tare da matarsa da kuma yayansa.

Ya ce masu garkuwar basu tuntube shi ba domin neman biyan kudin fansa.

“Basu bukaci kudin fansa ba daga wurin mu a gaskiya bamu samu tattaunawa da su ba amma mun shigar da korafi gaban jami’an tsaro,” ya ce.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin kasarnan da suke fama da matsalolin tsaro.

You may also like