Wasu Yan Kunar Bakin Wake  Biyu Sun Kai Hari kamaruWasu matasa biyu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai harin kunar bakin wake a kofar shiga kasuwar garin Mora da ke cikin kasar Kamaru inda aka girke sojojin hadin guiwa na kasashen Nijieriya, Nijar, Chadi, Kamaru da Nijeriya don yaki da Boko Haram
Wani mai taimakama gwamnan yankin Arewa mai Nisa, Midjiyawa Bakary ya ce mutanen da suka mutu sun hada da wani dalibi da kuma wata mata. Jami’in ya ce wasu mutanen biyar sun jikkata a harin.
Ya ce dan kunar bakin waken ya yi shiga irin ta almajiri ne, yayin da ya shiga kasuwar wacce ta cika da mutane saboda Kirsimeti. Jami’ai masu aikin sintiri sun hango shi kafin ya kaiga shiga cikin taron jama’a, amma bayan da aka tsayar da shi, sai ya tayar da bom din dake jikinsa.
A baya, ‘yan kunar bakin wake da ake zargi ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun sha kai hare-hare a garin na Mora, wanda ke nisan kilomita talatin daga iyakar Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan ikrarin gwamnatin Najeriya cewa ta fatattaki ‘yan Boko Haram daga Dajin Sambisa na jihar Borno. Kuma daman masana sun ce ‘yan kungiyar za su fantsama zuwa wurare daban-daban domin kai hare-hare.

You may also like