Wasu mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun yi kira da a tsige shugaban kasa Muhammad Buhari saboda amincewar da yayi na a fitar da kudi har dalar Amurika $496 ba tare da izininsu ba.
Hakan ya biyo wata wasika da Buhari ya rubutawa majalisar a ranar Talata, inda yake kare kansa kan izinin fitar da kudin da aka sayo jiragen sama samfurin Super Tucano daga kasar Amurka.
An ce cire kudin ne daga asusun rarar mai.
A cikin wasikar shugaban ya ce ya riga ya san cewa yan majalisar za su amince masa a kashe kudin wajen sayen jiragen.
Hakan da shugaban kasar ya yi ya harzuka wasu daga cikin yan majalisar inda suke ganin cewa kamar shugaban kasar ya take ikonsu na bawa bangaren zartarwar ikon kashe kudi.
Wasu daga cikin yan majalisar sun yi kira da a rubutawa shugaban kasar wasika domin sanar da shi cewa ya saba kundin tsarin mulkin kasa.
Kashe kudi ba tare da izinin majalisar kasa laifi ne da zai iya sawa a tsige shugaban.
Wasu da dama daga cikin yan majalisar sun goyi bayan tsige shugaban kasar.