
Asalin hoton, Getty Images
A karshen watan janairun 2023 aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a wasu kasashen Turai, sai karshen kakar nan za a ci gaba da hada-hada.
To sai dai kuma kamar yadda doka ta tanada kungiyoyi za su iya sayen, wadanda kwantiraginsu zai kare zuwa karshen kakar nan.
Kenan kungiya za ta dauki wanda yarjeniyarsa ta kusan karewa zuwa karshen kakar nan da wanda bai da wata kungiyar da yake da yarjejeniya da ita.
BBC ta yi duba na tsanaki kan wasu da za a iya dauka a yanzu haka
Isco dan kasar Spanin, mai shekara 30
Cikin ‘yan wasa da ke kasa a yanzu Isco shi ne wanda keda kwarewa da yawa, bayan lashe kofuna da yawa a Real Madrid
Dan kwallon tawagar Sifaniya ya lashe Champions League biyar da Club World Cup hudu da La Liga uku da Uefa Super Cup uku da Copa del Rey.
A cikin watan Disamba dan wasan da Sevilla suka amince kowa ya kama gabansa, an kuma sa ran a karshen Janairu zai koma Union Berlin daga baya batun ya bi ruwa.
Jerin wasu ‘yan wasan da za a iya dauka a wannan lokacin
Sime Vrsaljko dan kasar Croatia, mai tsaron baya, mai shekara 31.
Jese Rodriguez dan kasar Spain, mai tsaron baya, mai shekara 29.
Federico Fernandez dan kasar Argentina, mai tsaron baya, mai shekara 33.
Jordan Lukaku dan kasar Belgium, mai tsaron baya, mai shekara 28.
Bojan Krkic dan kasar Spain, mai cin kwallaye, mai shekara 32.
Jurgen Locadia dan kasar Netherlands, mai cin kwallaye, mai shekara 29.
Renzo Saravia dan kasar Argentina, mai tsaron baya, mai shekara 29.
Pape Cheikh Diop dan kasar Senegal, mai wasa daga tsakiya, mai shekara 25.