Wasu yan’uwa huɗu sun kashe kakarsu domin yin tsafin kuɗi a jihar Edo


Ana zargin wasu mutane huɗu da laifin kashe kakarsu mai shekaru 67 domin yin tsafin kuɗi a Benin babban birnin jihar Edo.

Yan’sanda sun bayyana sunan mutanen da ake zargi da suna Dickson Oluka, Salaye Oluka, Martins Oluka da kuma Austin Enayi.

An gano cewa mutanen sun aikata laifin ne a gida mai lamba 28 dake layin Asowota a unguwar Ohovbe Benin babban birnin jihar bayan da suka tuntubi wani mai maganin gargajiya.

Mai maganin gargajiyar an ce ya faɗa musu su rataye kunkuru mai rai a bayansu kana su kashe wani da yake kusa da su inda ya tabbatar musu cewa da zarar sunyi tsafin to za su yi kuɗi.

Mutanen da ake zargi da suka dawo gida sun hada baki ya junansu inda suka rataye kunkuru a bayansu kana suka rike kakarsu  suka buga kanta da jikin bango hakan yasa tace ga garinku nan.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwanbuzor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace biyu daga cikin mutanen da ake zargi Dickson da Salaye sun shiga hannun yan sanda yayin da Martins da Austin Enayi suka tsere tun daga ranar 12 ga watan Disambar 2017 lokacin da suka aikata laifin.

Yace yan sanda sun shiga farautar mutane biyun da suka tsere.

You may also like