Wata Aku Ta Fadawa Matar Gida Soyayyar Da Mijinta Yake Da Yar Aiki 


Da alamu dai dabbobi ma basa san karya da kuma aikata zina .domin kuwa saura kiris wata aku ta sa a garkame mai gidanta a gidan yari, bayan da ta bayyana wa matarsa cewa mijinta yana aikata lalata da yar aikin gidan. 

Akun ta tona asirin mai gidan ne ta hanyar,bayyana irin kalaman da yakewa yar aikin gidan a gaban matarsa, wacce tuni dama take zargi wani abu a tsakanin mijinta da kuma yar aikin. 

Tayi mamaki kan yadda mijinta,yake neman yar aikinta da lalata a gidansu dake Kuwait.

Idan aka tabbatar da laifin to mijin zai iya shafe shekaru a gidan yari, tare da aiki mai tsakani, matar dai tuni takai Akun wurin yan sanda a matsayin sheda.

Yan sanda sun ce maganar Akun baza ta iya zama shaida ba a gaban kotu, saboda baza a iya ganewa cewa taji maganar daga bakin Mijin matar ko kuma daga akwatin Talabijin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like