Hatsabibiyar Bokanya Baba Vanga Ta Yi Hasashen Trump Ba Zai Shiga White House Ba.
Wata makauniyar Bokanya da aka fi sani da Nostradamus wacce ta yi hasashen harin 9/11, Ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, Tasowar ISIS, Tsunami da kuma cin zaben Obama ta kara yin hasashen cewa Donald Trump ne shugaban kasar Amurka na karshe.
A cewar Bokanya Baba Vanga wani abu zai faru ga Trump kafin 20 ga Janairu 2017 da zai hana shi shiga fadar White House. Jim kadan bayan ayyana sunan Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka, magoya bayan Hillary Clinton suka fara gudanar da mummunar Zanga-zanga.