Wata Gobara Ta Lamushe Sashin Kamfanin yin Giya Dake LegasWata gobara lakume wani sashi na Babban kamfanin yin giya na ‘ Nigerian Breweries Plc’ da ke yankin Iganmu  a jihar Legas inda a halin yanzu jami’an kashe gobara suna ci gaba da kokarin shawo kan lamarin.
Rahotanni daga Legas sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da misalin Karfe biyar na safen yau Lahadi inda ta Lakume sashen da ake adana kayayyaki wanda ya kunshi har da kwalabe. 

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta kasa ta nuna cewa mutum uku ne suka samu raunuka a halin yanzu kuma an garzaya da su asibiti.

You may also like