Wata Kotu A Congo Ta Yankin Hukuncin Zaman Kaso Na Shekaru 5 Kan Shugaban Wata Jam’iyyar Adawa


60fa1702-3081-4caa-b02e-e0de0ff456ac

Wata kotu a kasar Congo Demecradia ta yankin hukuncin daurin shekaru 5 kan shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar bayan da ta kama shi da laifin tsare wasu sojojin kasar ukku a makon da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa kotun daure Franck Diongo a dai lokacinda gamayyar jam’iyyun adawar kasar suke kokarin cimma yerjejeniya da gwamnatin shugaba Josept Kabila na saukarsa a cikin shekara ta 2017 mai kamawa, kuma mai yuwa daure dhugaban jam’iyyar MLP ya kawo cikas a cikin tattaunawa.

Lauyan da ke kare Diongo ya bayyana cewa shugaban jam’iyyar ta MLP bai da lafiya kuma bai iya kare kansa a gaban kotunba, don haka wannan hukuncin da aka yanke masa tsagorin siyasa ce. Amma majiyar gwamnatin kasar ta Congo a birnin Kinsasa ta musanta cewa akwai ra’ayin gwamnati a cikin hukuncin  kotun.

You may also like