Wata Kotu a  kasar Libiya ta wanke dan marigayi Gaddafi daga zargin kisan kai 


Wata kotun daukaka kara a  kasar Libiya ta wanke daya daga cikin ƴaƴan tsohon shugaban kasar Kanal Mu’ammar Gaddafi bisa tuhumar da ake yi masa na kashe wani dan kwallon kafa kafin juyin juya halin kasar a shekarar 2011.

Saadi Gaddafi wanda ake tsare da shi a babban birnin kasar Tripoli tun bayan da aka tasa keyarsa daga kasar Nijer a shekarar 2014, ba a same shi da laifin ” kisan kai, yaudara, barazana, bauta da kuma bata sunan tsohon dan wasan kwallon kafar, Bashir Rayani,” a cewar  ma’aikatar shari’ar kasar.

Ma’aikatar ta ce an ci tarar saadi dinari 500 kwatankwacin dalar Amurika 377 bisa samunsa da laifin mallaka da kuma shan giya a shekarar 2006.

Sa’adi wanda ya kasance dan kwallon kafa a lokacin mulkin mahaifinsa inda ya buga wasanni a kasar Libiya da kuma Italiya kuma ya kasance kwamandan rundunar sojin kasar ta musamman, har yanzu yana fuskantar tuhume-tuhume a Tripoli.

You may also like