Wata Mace Ta Haihu A Tashar Jirgin Kasa


Wata mace a kasar Afirika Ta Kudu, ta haihu a tashar jirgin kasa bayan da asibitoci biyu suka ki yarda su karbeta a cewar kafar yada labarai ta IOL dake kasar. 

Kafar yada labaran tace , asibitocin sun ki karbar matar mai suna Francine Ngalula, saboda matsayinta na me neman mafaka a kasar. 

Matar tace asibitoci biyu ne suka ki karbarta a birnin Pretoria, shine ta hau jirgin kasa zuwa birnin Johannesburg. Ta shafe mintuna 45 tana amai a cikin jirgin yayin da sauran fasinjoji suke kokarin iyawarsu wajen taimaka mata.

Lokacin da jirgin ya tsaya a tashar birnin na Johannesburg da misalin karfe 7:00 na safe, matar ta shafe sa’o’i biyar tana nakuda inda nan take ta haihu a dandamalin tashar.  

You may also like