Wata Mata Ta Ƙone Gidan Mijinta Ƙurmus Saboda Zai Mata Kishiya


Wata matar aure a garin Birnin Kebbi na jihar Kebbi mai suna Zainab, ta bankawa gidan mijinta wuta da tsakar daren jiya, inda gidan ya kone kurmus ba’a tsira ko da tsinken susar kunne ba, saboda auren da mijin yake da niyyar yi wanda aka shirya daura shi a yau bayan sallar Juma’a.

Wani makwabcin gidan su Zainab din ya shaidawa wakilinmu cewar, mijin matar mai suna Yunusa ya shirya tsaf domin karin aure na wata yarinya budurwa makwabciyar su mai suna Aisha, kuma komai ya kankama inda aka sanya wannan rana ta Juma’a a matsayin ranar daurin aure, kuma ance Malam Yunusa yayi goma sha tara ta arziki ga Uwargidan tashi domin taji dadin tarbar kishiyar da za’a yi mata, sai dai abin takaici kishi ya hana Zainab daurewa.

Lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘Yan sandan Jihar Kebbi DSP Mustafa Suleiman, yace labarin wannan ta’asa bata zo garesu ba tukuna, amma za su gudanar da bincike a kai, lamarin ya faru ne a yankin Badariyya dake Birnin Kebbi.

You may also like