Wata Mata Ta Haifi Jariri Mai Kai Biyu A LegasWata mata ta haifi jariri mai kai biyu a yankin Ogudu da ke cikin jihar Legos inda tuni aka garzaya da shi asibitin koyarwa na jami’ar Lagos don ci gaba da gudanar da bincike game yanayin halittarsa.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Talata ne aka kai Matan asibitin Mid-In da ke kan titin Oshogbo domin haihuwa. A cewar Shugaban asibitin, Dora Moses binciken da suka gudanar ya nuna cewa za ta haifi ‘yan biyu ne amma bayan ta sauka lafiya sai aka tarad jariri ne da kai biyu.

 Ya ce an sha samun  irin wannan a kasar Indiya amma kuma ba a iya raba su saboda kawunan a jiki guda suke.

You may also like