Wata mata a jihar Cross Rivers ta haifi ‘yaʼya biyar bayan fama da rashin haihuwa na tsawon shekara goma.
Matar ta haifi ‘ya’ya biyar din ne a lokaci guda a asibitin Jamiʼár Calabar. A cikin yaran da aka haifa, an samu namiji biyu da mata uku.
Mahaifin yaran, mai suna Dr. Ekpo Edet, ya nuna matukar farin cikin sa, inda ya ce “Ina godiya ga Allah domin albarkar da ya yi mana. Wannan haihuwa na yara biyar a lokaci guda shi ne na farko a tarihin Jihar Cross River.
Matar Gwamnan Jihar Cross River, Dr Linda Ayade, tana cikin mutanen da suka kai ziyara da gaisuwa. Ta nuna farin-ciki ga wannan haihuwan da aka yi. Inda bayan ta gama jawabi, ta baiwa mejegon kyautar naira milyan daya. Bugu da ƙari, ta yi ma maʼaikacin asibiti masu kula da haihuwa kyautan kuɗi N500,000 domin koƙarin da suka yi wajen haihuwa.
Manyan mutane sun ta kai ziyara zuwa wajen haihuwar.