Wata Mata Ta Halaka Mijinta Ta Hanyar Burma Masa Wuka A CikiA yammacin ranar Alhamis din da ta gabata ne wani magidanci mai suna Ibrahim Ismail wanda aka fi sani da Iro dake garin Numan jihar Adamawa ya hadu da ajalinsa, inda matar sa mai suna Halima ta burma mai wuka a gefen hakarkarinsa. Wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwansa.

A yayin zantawa da wani abokin marigayin mai suna Dalladi da wakilinmu ya yi, ya sheda cewa marigayin ya bar su  wajen sana’ar su na saida mai a tashandom, inda ya tafi gida don ya kai cefane. Koda ya iso gida ya iske matarsa Halima ba ta gida ta dan fita. Sai ya ajiye cefanen ya tafi bai yi nisa ba, ya sake dawowa. Koda ya dawo sai ya iske ta tana yanka kubewar da ya kawo.

Abokin mamacin ya kara da cewa daga bisanin mijin ya hau matar ta sa da fada akan fitan da take yi ba tare da ta tambaye shi ba. Hakan ne ya sa abu ya cabe musu, inda ya kai duka ita kuma ta kawo masa suka da wuka, kamin ya kare ta kai masa suka. Nan dai ya yi ta neman agaji har rai ya yi halinsa. 

Marigayi Ibrahim Iro dai ya mutu ya bar da daya da ciki.

You may also like