Wata Mata Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Kwana 14 Da Fiya FiyaWata mata mai suna Hindatu Abdullahi ta hallaka dan kishiyarta ta hanyar shayar da shi sinadarin fiya-fiya “A ranar 19/8/2017 jami’anmu sun samu rahoto a gidan wani mai suna Abudullahi Ori dake kauyen Wuro Bogga, Duguri a karamar hukumar Alkaleri, wanda a yanzu haka ya tafi aikin hajji ya kuma bar matansa su biyu a gida  Fatima Abdullahi uwar gida, da Hindatu Abdullahi amarya. Ita amarya mai suna Hindatu ta shiga dakin uwar gida inda ta dauki danta mai suna Muhammad Abdullahi mai kwanaki 14 kacal a duniya inda ta bashi fiya-fiya a dakinta, a yayinda ya suma bayan da aka yi kokarin garzaya da shi asibiti yaron ya mutum”. In ji Datti 

A zantawarmu da ita Hindatu Abdullahi wacce ta amsa laifinta sai dai ta bayyana cewar tun usuli auren dole ne aka yi mata da shi wannan mutumin mai suna Abdullahi Ori “Akwai wanda na ke so, har an daura mana aure da shi a kotu babana ya ki amincewa duk gidanmu har ‘yan uwana kona na sona da shi, nima ina sonsa, Babana ne kadai baya sonsa ya dage aka aura min wannan alhajin, kuma gaskiya ina shan azaba sosai a gidansa, na rasa yanda zan yi tsautsayi ya kwasheni na aikata wannan mummunar aika-aikar”. In ji Hindatu

Ta kara da cewa ita gaskiya ba tsananin kishi bane ya sanyata wannan aika-aikar illa dai kawai yanda uwar gidan ta rabata da mijin gabaki daya a yayin zamantakewar aurensu “Ni ina gidan ne kawai ina zaman gida, amma idan na je na fada wa babanmu halin da na ke ciki sai ya koreni ya dauki bulala ya dukeni ya ce karya na ke yi”. In ji wacce ta hallaka jaririn kishiyarta.   

You may also like