Dandazon jama’a ne suka cika ofishin ‘yan sanda dake garin Ayingba a karamar hukumar Dekina ta jihar Kogi, don ganin yadda za ta kaya kan wata ma’aikaciyar asibiti da sabuwar jaririyar da aka haifa ta bace a karkashin kulawarta.
Lamarin wanda ya auku a ranar Lahadin da ta gabata a asibitin Peniel dake garin na Ayingba, mai jegon mai suna Joy Idah Mudi, ta bayyana cewa bayan ta haihu an raba musu daki ne da jaririyar, inda daga bisani da aka kuma ma’aikaciyar lafiyar da jaririyar ke karkashin kulawarta ta fito da jaririyar, ta bayyana cewa ba ta san inda jaririyar ta shiga ba.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, ma’aikaciyar asibitin na hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincikenta kan yadda aka yi jaririyar ta salwanta.