Wata Mata Ta Yankewa ‘Yarta Hannu saboda Tana Fitsarin Kwance


Kusan mako guda da ya wuce ne a jihar Bayelsa wani Mr Benjamin ya kone diyarsa mai shekaru 4 da haihuwa da abin tafasa ruwan zafi, domin ta yi fitsarin kwance.
Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa wata mata mai zama a birnin tarayya Abuja ta ci zarafin diyar ta akan irin wannan dalili na fitsarin kwance.
A cewar mujallar Daily post, matar mai suna Chioma, daga jihar Ebonyi nada yara guda hudu kuma tana zama tare da dukkan yaran nata a yankin Apo dake Abuja.
A cewar Mrs Dorathy Njamanze, ‘yar rajin kare hakkin bil’adama, ranar 22, ga wannan watanne suka sami labarin yarinyar da mahaifiyarta ta kusa guntule mata hannu a matsayin horo sakamakon ta yi fitsari a kwance, ta kara da cewa sun garzaya gidan inda suka hadu da sauran ‘ya’yan matar, da makwabtanta da kuma Kyamins din da ya taiamakawa yarinyar da taimakon gaggawa kafin a kaita asibiti.
Dorathy ta ci gaba da cewa “ matar ta yanke fatar hannun diyar tata ne, kuma ta ci gaba da yankawa har ta kusa tarar da kashi sai makwabta suka kaiwa yarinyar dauki.
Yanzu haka Chioma tana hannun ‘yan sanda, hukumar kula da hakkokin yara kuma ta mika yarinyar ga dangin matar har sai an kammala binciken mahaifiyar tata.
Kuma an yi mata dinki a hannun da mahaifiyar tata ta kusa guntule mata.
Daga karshe ta bayyana cewa “an taba kai karar matar akan irin cin zarafin da Chioma take wa ‘ya’yanta, inda aka tsare ta na wani dan lokaci sa’an nan aka sake ta. Dalili kenan na rashin sanin lokacin da Chioma za ta fito daga hannun jami’an ‘yan sanda a wannan karon.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like