Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a yankin Nasr da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar a jiya Juma’a.
Majiyar watsa labaran Masar ta sanar da cewa: Wata mota da aka makare da bama-bamai ta tarwatse a yankin Nasr da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar amma babu hasarar rai ko jikkata.
Wata majiyar tsaro a birnin na Alkahira ta bayyana cewa: Tarwatsewar motar ta zo ne a daidai lokacin da motar wani alkali ke shigewa a yankin, lamarin da ke nuni da cewa akwai yiyuwar an yi nufin halaka alkalin ne, amma dai harin bata ritsa da shi ba.
Tarwatsewar motar ta janyo hasarar dukiyoyi musamman na motocin da suke kusa da inda aka ajiye ta, don haka jami’an tsaron Masar sun fara gudanar da bincike kan lamarin.