Wata Mota Makare Da Barasa Ta Fada Cikin Masallaci


Wasu masallata sun tsallake rijiya da baya, bayan da wata mota makare da barasa ta afka Babban Masallacin Juma’a na Gaji dake Olonkoro akan hanyar Igbona a garin Oshogbo ta jihar Osun. 

Shedun gani da ido sun ce motar ta kwace ne inda ta afka cikin masallacin yayin da mutane suke Sallah.

Kwalaben giya duk sun bata kan titi da kuma harabar masallacin yayin da ruwan giya ya watsu a ko ina hakan ya bata ran masallata.

 Lamarin ya harzuka masallata sai da aka dau tsawon lokaci malamai da kuma wasu manyan gari suna bada hakuri a kokarin hana lamarin zama wani gagarumin rikici.

 Rundunar yan sandan jihar ta Osun tace ta samu rahoton faruwar lamarin, a cewar kakakin rundunar Folasade Odoro.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like