Wata Sabuwa Kungiyar Shi’a Ta Bulla A BornoHukumar Tsaron lafiyar farar hula ta kasa ( NSCDC ) ta gano wata sabuwar kungiyar Shi’a a karamar hukumar Kwaya Kusar da ke jihar Borno wadda koyarwarta ya bambanta da na bangaren Malam Ibrahim El Zakzaky.
Kwamandan hukumar na jihar, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da cewa sun gayyato Shugaban sabuwar kungiyar wanda ya nuna masu cewa kungiyarsa ba ta koyar da ta’addanci. Shugaban hukumar ya kuma jaddada cewa za su lamunci wata Kungiya a jihar wadda za ta iya haifar da irin rikicin Boko Haram wanda har yanzu ake kokarin kwantar da shi.

You may also like