Wata Sabuwa: Majalisa Na Shirin Yin Dokar Samar Da Kariya Ga Barayin Gwamnati Majalisar Wakilai ta fara nazari kan wani kudiri wanda zai ba barayin gwamnati kariya daga fuskantar shari’a idan har sun cika sharuddan da ke cikin tanade tanaden kudirin.

Kudirin dai ya tanadi cewa duk wani barawon gwamnati wanda ya gabatar da kansa kuma ya biya haraji daga kudaden sannan kuma ya kafa wata masana’anta da kudin ta yadda zai amfani al’umma.

You may also like