Wata Yar Arewa Musulma Ta Bude Tashar Talabijin Ta Yanar Gizo


A yayin da ake korafi game da karancin samun kafafen yada labarai mallakar ‘yan Arewa da za su rika gogayya da na ‘yan kudu, wajen samar da ingantattun labarai game da gaskiyar abubuwan da ke faruwa da al’ummar wannan yanki, an samu wata mace Musulma da ke zaune a garin Jos, wacce ta bude wata tashar talabijin ta RoTV, wato Rasheeda Online TV.

Wannan tasha a cewar jagorar tafiyar Hajiya Rasheeda Noro Yahaya za ta rika samar da labarai ne da sharhi kan al’amuran yau da kullum da harshen turanci, domin zama taga da ‘yan kudu da duk wasu masu neman fahimtar abubuwan da ke faruwa a Arewa za su samu gaskiya bayanan da suke nema.

Kuma kasancewarta mace, Hajiya Rasheeda ta ce RoTV za ta mayar da hankali wajen bayyana irin cigaban rayuwar da matan Arewa ke samu a bangaren ilimi, siyasa, kasuwanci, da shugabanci da kuma nauyin tarbiyyar al’umma da ke kanta.

You may also like